Dalilin Da Ya Sa Aka Dakatar Da Itikafi A Masallacin Abuja

Sakamakon ce-ce-kucen da ya biyo bayan dakatar da Itikafi a Masallacin kasa da ke Abuja da Hukumar Masallacin ta yi, Aminiya ta tuntubi daya daga cikin limaman masallacin Dokta Muhammad Kabir Adam inda ya yi bayani a kan dalilan da suka yi haka da kuma irin matakan da suke shirin dauka kafin bai wa jama’a damar yin Itikafin a badi.
An samu sauye-sauye a tsarin gudanar da masallacin nan ko za ka yi mana bayani a kan wasu daga cikinsu? To Alhamdulillahi muna gode wa Allah Madaukakin Sarki, shugabancin wannan masallaci a halin yanzu yana karkashin Babban Murshid na masallacin, wanda shi ne shugaban masallacin baki daya wato daga kan limamai har zuwa bangaren gudanarwa da ya kunshi sauran ma’aikatan masallacin. Shi ne Farfesa Shehu Ahmad Sa’d Galadanci, wanda shi ne Shugaban Makarantar Koyar da Larabci (SAS) da ke Kano na farko bayan tafiyar Larabawan da suka kafa makarantar tare da shugabantarta na tsawon shekaru. shi ne kuma farkon Shugaban Jami’ar Usman dan Fodiyo da ke Sakkwato. Ya yi Jakadan Najeriya a Saudiyya, kuma ya yi Kwamishina na kasa a Hukumar Zabe ta kasa (INEC). Mutum ne wanda ya shugabanci wurare daban-daban kuma yanzu Allah Ya kawo mana shi nan Babban Masallacin kasa a matsayin Murshid kuma alhamdulillahi an samu sauye-sauye masu ma’ana da dama bayan zuwansa. Muna fatan Allah Ya ci gaba da yi masa jagora. Kwatsam sai ga labarin dakatar da Itikafi a wannan masallaci a bana, mene ne dalili? Al’amarin I’itikafi kamar yadda yawanci aka sani ibada ce ta musamman wacce aka fi yin ta a lokacin azumin watan Ramadan kuma musamman a goman karshe kamar yadda malamai musamman na Mazhabar Malikiyya suka fi karfafawa cewa a yi ta ana azumi ko da ba na Ramadan ba ne. Kuma wannan Sunnah ce ta Manzon Allah (SAW) kamar yadda aka ruwaito shi yakan tare a masallaci dungurugum a duk lokaci irin wannan. Kuma haka ake yi a wannan masallaci tun 1992 bayan bude shi a 1991. Sai dai a lokacin jama’ar da ke yi ba su da yawa ta yadda aka dauki nauyin jama’ar da ke zuwa ba tare da samun wata damuwa ba. To a bana sai muka kula da yadda matsalar ke ta karuwa inda kuma ake bukatar karin tanade-tanade don ganin an tafiyar da ibadar a cikin tsari kamar yadda shari’ar Musulunci ta tanada. Kuma kamar dai yadda muka ga ake gudanarwa a wasu kasashen musulmi na duniya. Zan ba da misali da wani masallaci a birnin Jiddah na kasar Saudiyya mai suna Masjidur Raajihi. Masallacin yana tanadar dukan abubuwan da mai I’itikafi ke bukata saboda sun san adadin wadanda za su zo ta yadda ba za su fi karfin tanadinsu ba. Matakin da suke dauka kuwa shi ne suna raba fom tun kamar wata biyu zuwa uku kafin Ramadan duk wanda yake bukata ya cika. To mu ma a yanzu ya zama wajibi mu dauki irin wannan tsari a matsayinmu na Babban Masallacin kasa don ganin an karbi baki gorgodon karfin wurin. Babu dadi ka ga masu I’itikafi sun takura har a wajen makewayi ana layi ga kuma matsalar sace-sace da ake yi musu. To a dalilin haka ne muka ga ya zama dole mu dakatar da karbar masu I’itikafi a nan masallacin a bana, sannan za mu yi cikakken tanadi kafin badi idan Allah Ya kai mu. Daga cikin matakan da za mu dauka da farko za mu so mu san adadin masu zuwa don tanadar wajen ajiyar kaya ga kowannesu da kuma bashi mabudin akwatinsa ta yadda ba za a sace masa ajiyarsa ba. Sai kuma sanin daga inda mai I’itikafin ya fito sannan idan wani abu ya faru da shi wa za a nema. Ka ga wadannan tanade-tanade ne da ba za su yiwu ba a dan kankanen lokaci. Dalili ke nan da ya sa muka bai wa jama’a hakuri har sai badi insha Allahu. Misali duk wanda zai zo sai ya cika fom tun kamar wata biyu ko uku kafin lokacin tare da cikakken sunansa da adireshinsa da wadanda suka tsaya masa a cikin fom din. Mu kuma mu tanadi duk abin da za su bukata ciki har da wuraren wanka da bahaya da akwatunansu da ma’aikata na musamman da ba na yau da kullum ba don kula da bukatunsu kamar dai yadda yake faruwa a masallatan Harami na Makka da Madina. Kuma akwai yiwuwar a yi musu jakunkuna watakila ma har da sutura ta bai-daya (yunifom) don saukin bambance su da sauran jama’a, sannan su kuma su samu sukunin bauta wa Allah a cikin natsuwa da kwanciyar hankali. To ganin lokaci ya kure wadannan tanade-tanade ba za su yiwu ba ne ya sa muka dage sai badi insha Allahu. Wadansu na danganta lamarin da zanga-zangar ’yan Shi’a, alhali ko lokacin hare-haren Boko Haram ba ku dakatar ba, me za ka ce? Wannan ba shi ne dalili ba, illa dai matakin gyara ne ake so a dauka. Sanin kowa ne ko da wuraren kewayawa ne suka yi karanci sai an samu matsala, kuma a dalilin haka sai ka ga fitsari a ko’na, bahaya a ko’na kuma a cikin masallaci. Ka ga wannan bai daidai ba ne zai iya kawo barkewar annobar cututtuka, ga kuma matsalar sace-sace da na gaya maka, da sauransu. Babu batun zanga-zangar ’yan Shi’a a lamarin. ’Yan shi’a mu a wajenmu Musulmi ne mazhabarsu suke bi, kuma dama a Musulunci akwai mazhabobi daban-daban ciki har da na Shi’a. Yaya batun masu zuwa daga wasu garuruwan Abuja shin akwai yiwuwar dakatar da su ko su ma za a bar su a lokacin? To idan lokacin ya yi kamar yadda na yi bayani za a raba fom duk mai bukata sai ya cika, sannan idan adadin da masallaci ya ga zai iya dauka ya cika sai a rufe dauka a bai wa sauran mutane hakuri. Maganar masu zuwa daga wasu garuruwa ai wata mas’ala ce ta shari’a. Hadisin Manzon Allah (SAW) ya ce ba a daura damarar tafiya wani masallaci domin ibada daga wani gari sai dai daya daga cikin masallatai uku, wato Masallacin Harami na Makka da na Madina sai kuma na Aksa da ke Birnin kudus. Ka ga abu na shari’a dama tun farko ya kamata mai I’itikafi ya yi la’akari da shi ba sai an gaya masa ba. A shari’ance wannan Masallaci na kasa da na Enugu da na Kano da na Akwa-Ibom duk sunansu masallaci kuma matsayinsu daya ne a wurin Allah babu wanda ya fi wani. An san masallatai da tanade-tanade kamar kula da marayu da ayyukan da’awa da sauransu, a matsayin wannan masallaci na kasa ko akwai irin wannan tsari? Wannan masallaci yana da hanyoyi daban-daban da yake taimaka wa al’umma, misali ko a yau bayan tafsiri na mata da ake yi da safe an raba kayan abinci iri-iri ga mabukata. Sannan wadansu suna zuwa da matsalolinsu a taimaka musu a wannan lokaci, har kudin makaranta na marayu idan bukata ta taso sai a ba su. Haka nan ana ayyukan da’awa a nan da kuma zuwa wasu wurare baya ga wasu kungiyoyin da’awa akalla biyu da aka ba su ofishi a nan, aikinsu ke nan a kullum, wato Muslim Professionals in Da’awa (MPD) da kuma Abuja Center for Islamic Propagation, ga kuma Jama’atu Nasril Islam.

No comments:

Post a Comment