ME YA RABA RARARA DA BABAN CHINEDU?

Abokin damo, guza! A sanadiyyar siyasar APC ce dangantar Dauda Kahutu Rarara da Abokinsa Baban Chinedu ta kara karfi sosai, duk da yake daman 'Yan Jiha daya ne Wato katsina, kuma daga yanki guda suka fito a shiyyar Funtua, Amma dai Dalilin Siyasa yasa suka cure waje daya suka zama Danjuma da Dan jummai.


Hakan kuwa ya samo asali tun farkon yakin neman zabe lokacin da mawakan Hausa na Siyasa kowa ya murza kambunshi,  Duk da yake kowanensu ba boyayye bane a fagen waka, Amma dai Wakar nan da suka yi tare mai taken "Mako Shidda zai zo ai zabe" itace ta kara daga darajarsu saboda wakar tayi yawo a Gari kamar Wuta bazara.

Bayan nan kuma suka zo suka sake yin wakar nan ta Masu Gudu Su Gudu, ita ma ba karamin karbuwa tayi ba, Daga nan ne fa aka fara tunanin mutanen nan kakarsu ta yanke saka.

Sanin kowa ne a wancan lokacin duk wani yakin neman zabe ko kuma Taron Siyasa na Jam'iyyar APC da a ka yi a baya da su a ka yi, kuma  akan gansu sun shigo mota daya kuma idan suka zo wajen taron wuri daya zasu zauna, bugu da kari mutane a tare suke ganinsu suna waka a wajen Taro.

Amma abin mamaki ga dukkan wanda ya san mawakan zai fahimci a wannan lokacin akwai sabanin da ya shiga tsakaninsu domin ruwa baya tsami banza!

Saboda irin yanda yanzu kowa ya kama gabanshi yana huddarsa shi kadai. Kuma mutane sun saurari sabuwar wakar Rararada  yayi wakar mai taken  "Malam yaci kudin makamai" babu Baban Chinedu a cikinta, shima kuma Baban Chinedu yayi sabuwar wakarsa ta "Masu gudu Su tsaya" ba'aji muryar Rarara a cikin ta ba

Sannan a wannan lokacin ba'a ganinsu Tare, Koda kuwa wurin taro aka gayyatosu a yanzu zaka gansu kowa yazo daban kuma ba wuri daya suke zama ba, Sannan kowannensu zai yi wakarsa daban, sabanin irin yanda sukeyi a can baya.

To, yanzu dai mutane sun fara sake-sake a zuciyoyinsu akan Me ya hada Baban Chinedu da Rarara?

Sai dai wasu suna ganin akasin da aka samu tsakaninsu bai wuce na makudan kudin da akace an basu a kasar nijar  a shekarar da ta gabata. Wanda wajen raba kudin ne aka samu matsala domin Rarara yana ganin kamar shine ogan Baban Chinedu don ko babu shi yayi waka yana ganin za ta tashi, kamar ma makalashi ne ya ke yi a wakar don haka dole kasonshi wajen raba  kudi yafi na Baban Chinedu

Wata majiya ma ta tabbatar wa da wakilinmu cewa anga Baban Chinedu a ofishin Rarara suna zage-zage Wanda sai dai aka samu da kyar aka kashe wutar hayaniyar tasu domin sai da sukayi uwar watsi.

A Gefe guda kuma wasu suna ganin rigimar tasu ta samo asaline sakamakon Rashin jituwar da aka samu tsakanin Rarara da Adamu Zango, inda Rarara ya kalubalanci Zango akan wai Ashe sun shirya da Ali Nuhu bai fada masa ba. Shi kuma Baban Chinedu ya nunawa Rarara bai kamata yayi fushi da Zango ba, wasu suka ce sanadiyyar babewarsu kenan.

Amma mafi yawan mutane sunfi ta'allaka Rigimar tasu sakamakon Bambanci Ra'ayi da ya shiga tsakaninsu lokacin da Jam'iyyar APC a Jihar Kano ta da re gida biyu Wasu suka bi layin kwankwaso wasu kuma suka bi bangaren ganduje, To anan akace Rarara ya zabi yabi layin Ganduje, Baban Chinedu kuma ya zabi bangaren kwankwaso to anan ne suka samu sabanin fahimta tsakaninsu.

Mutane da damai dai kowa da irin abin da yake fadi akan rashin jituwar Rarara da Baban Chinedu wannan yace abu ka za ne ya hadasu. Wancan kuma yace A'a abu ka za ne ya hadasu. 


Wannan dalilin yasa wakilinmu bai yi kasa a guiwa ba, ya tuntubi Baban Chinedu akan ko minene ya hadasu da Rarara aka daina ganinsu tare? Sannan kuma  me zai Iya cewa akan sabanin da aka ce sun samu tsakaninsu da Rarara? da kuma jita-jitar da akeyi akansu sai yace:

To kasan ita Rayuwa idan kuna da daukaka shine zaka ji mutane na jita-jita akan ku. Amma Tsakanina da Rarara sai Allah, Ni dashi tub da taya Ne. Abokan juna Ne, Sana'armu daya, to idan ma muna wani rikici Wanda ya shafemu ne, bai shafi Wanda mutane ke cewa mun bata tsakaninmu ba.

Yana da izini yayi Ra'ayinshi nima ina da ra'ayina.  Tun da bashi ya koya min waka ba. Nima kuma bani na koya masa ba, kaga kenan kowa yana da ra'ayinshi. Kuma Allah na tuba ai fada abune na yarinya ta, ni mai zai kai ni sutudiyon Rarara har muyi fada dashi, kamar dai wasu kananan yara.. Ina tabbatar maka da cewa yanda mutane ke daukar abun bai kai haka ba.

Sannan ina kara tunatar da mutane cewa kowa yana da Ra'ayin kansa a tsakaninmu. Kuma da kwankwaso da ganduje duk tushe daya ya daukosu,  Sai dai ni yaron kwankwaso ne kuma ko Rarara ya sameni da kwankwaso. Kaga idan yazo yana ra'ayin ganduje nasan ra'ayinshi ne. Amma ni dai tifikal yaron kwankwaso ne, kuma maganar cewa yanzu mun daina waka tare ko kuma ba'a ganinmu wuri daya ai ya kamata mutane su tuna baya da can din aiba tare muke ba, kowa nashi yake yi har muka hadu muke waka tare saboda tafiyarmu da ra'ayinmu yazo daya. Kuma ko a da can din idan munje wajen taro ai kowa yana wakar sa.

Amma ina kara tabbatar maka da cewa Wata rigima ta ra'ayi daban, tarayyarmu dashi daban. Waccan hudda kuma wadda ta shafi rigimar siyasa daban. Kuma ba yau muka fara irin haka dashi ba, mun ma taba yi a baya, Inda yanayin wani ni kuma inayin wani Wanda tsakanina dashi ne. Kuma muka dawo muka ci da huddarmu

 Abu biyu ne Wanda zai Iya rabamu dashi shine ya dauki Wata jam'iyya wadda ba APC ba, ko kuma ni na dauki wadda ba ita yake yi ba, Amma maganar ace wai muna rigima bamu jituwa tsakaninmu ko kuma kudi ya hadamu dashi wannan kawai maganganu ne na mutane.

No comments:

Post a Comment