TASHIN GOBARA: GWAMNATIN KANO TA BADA GUDUNMAWAR N1.6B GA ‘YAN KASUWA

Gwamna Abudullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya raba Naira miliyan dubu daya da miliyan dari shida ga ‘yan kasuwar da gobara ta yi wa barna a jihar.
Kwamishinan yada labarai da harkokin matasa da kuma al’adu na jihar, Muhammad Garba ne ya bayyana hakan, inda ya ce sama da ‘yan kasuwar kantin kwari da Sabon Gari da Singa da kuma Kurmi dari biyar ne za su amfana da wannan bashi bayan an tantance su.
A wajen wannan bikin bada wannan gudunmawa gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnati ta bada wannan tallafi ne ga ‘yan kasuwa, domin su rage radadin hasarar da suka yi.
Ya jinjina wa ‘yan kasuwar a kan yadda suka yi kokarin gyara shagunansu da kansu bayan da gobara ta lakume su.

No comments:

Post a Comment