Ya Kashe Ɗansa, Yayin Daya Kama Shi Turmi Da Taɓarya Yana Aikata LuwaɗiWani mutumi mai suna Wendell Melton dan shekara 52 ya dankara ma dansa, mai suna Giovanni harsashi,a lokacin daya kama shi yana luwadi, inda nan take yace ga garinku a kasar Amurka. Shi dai Giovanni mai shekaru 14 ya tsunduma cikin halin luwadi ne tun ba yanzu ba, kamar yadda tsohuwar marikiyarsa ta bayyana. Sonja Jones tace “Mahaifin Giovanni ya dade yana muzguna ma yaron.”
Sai dai ta kara da cewa, mahaifin baya kaunar halin luwadi da yaron nasa ke ciki, inda hakan yayi sanadiyyar yawan samun takaddama a gidan nasu, tsakaninsa da yaron nasa.
“Na san Melton baya jin dadin halun yaron nasa, kuma na tabbata ya gwammace yaron ya mutu da a ce yana luwadi.” Jone ta kara da cewa rahotannin da ta samu sun bayyana cewa mahaifin Giovanni ya shiga dakin yaron nasa a lokacin daya kama shi tare da abokinsa suna luwadin, ganin haka ya dauki bindiga ya bindige shi.
Amma fa a nata bangaren, matar tace bata ji dadin kisan gillar da Melto yayi ma Giovanni ba, don haka take fatan kotu ta yanke masa mummunan hukunci, kuma ta daure shi har iya rayuwarsa.

No comments:

Post a Comment