Aikin hajji: Anyi ruwa da iska mai tsakani a Saudiya


Kamar yadda aka wallafa a shafukan sada zumunta anyi  iska da ruwan sama a Makkah da Arafat da Mina da kuma Muzdalifah.

An samu guguwa da iska mai tsanani da ruwan sama a Makkah yayin da mahajjata suka tare filin Mina dake wajen garin Makkah gabanin garzawa wajen filin arafa.

Lamarin dai ya faru  daren ranar lahadi 19 ga watan Agusta inda ta  ta lalata wasu runfunan alhazzai a Mina.
Bayan haka iskar ta daga rigar dakin ka'abba.
Kamar yadda aka wallafa a shafukan sada zumunta anyi  iska da ruwan sama a Makkah da Arafat da Mina da kuma Muzdalifah.

Yau Litinin 9 ga watan Dhul hijja mahajjata zasu gudanar da kololuwar aikin ibada wajen rayuwar arfa.
Wasu na hasashe cewa iskar da ruwan saman da aka yi zata rage zafi tare da baiwa mahajjatan damar yin ibadar cikin sanyi.
Bana dai akalla musulmai miliyan biyu suka tafi aikin hajj, yan Nijeriya dubu hamsin da biyar suka tafi gudanar da aikin ibadar bana.

No comments:

Post a Comment