Aikin hajji bana: Yar Nijeriya daga jihar Kano ta rasu a kasar Saudiya

Nigerian female pilgrim dies in Saudi Arabia

Shugaban fanin kula da lafiyar mahajjata ta hukumar NAHCON Dakta Ibrahim Kana ya tabbatar da hakan yayin da ya gana da manema labarai a garin Makkah

Hukumar hajji na Nijeriya NAHCON ta sanar cewa wata yar Nijeriya daga jihar Kano ta rasu a kasa mai tsaki gabanin fara aikin hajji na bana.

Shugaban fanin kula da lafiyar mahajjata ta hukumar NAHCON Dakta Ibrahim Kana ya tabbatar da hakan yayin da ya gana da manema labarai a garin Makkah.

Likitan hukumar yace marigayyar sananniya ce a wajen su domin tana fama da ciwon suga ta Diebitis kuma hukumar ta zarce da ita babban asibitin King Fahad inda a nan ajalin ta ya cika.

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai ta NAN ta ruwaito, marigayyan yar asalim karamar hukumar Ungogo dake nan jihar Kano ne.

Sai dai hukumar dai bata sanar da sunanta ba saboda bata sanar da iyalen ta game da lamarin.

 

No comments:

Post a Comment