Aisha Buhari: Uwargidan shugaban kasa ta samu digirin girmamawa a kasar Koriya ta kudu

Uwargidan shugaban kasa ta samu digirin girmamawa a jami'ar Sun Moon

Jami'ar Sun Moon dake Koriya ta kudi ta karrama Aisha Buhari da digirin girmamawa ranar asabar 11 ga watan Agusta.

Uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta samu digirin girmamawa daga jami'ar Sun Moon dake garin Asan nan kasar Koriya ta kudu.

Jami'ar ta karrama ta da digirin a fannin iliminn nazari da fasaha ranar asabar 11 ga watan Agusta.

Ta wallafa hotuna daga bikin girmamawan a shafin ta na Instagram tare da yin godiya ga Allah bisa karramawan da ta samu.

 

Tayi ma shugaban makarantar Dr. Sun-Jo Hwang tare da sauran mai'aikata godiya.

Aisha Buhari tace ta sadaukar da girmamawan ga mata da yara dake Nijeriya.

Mai dakin shugaba Buhari ta shahara a bangare kula da walwalar mata da yara kanana a Nijeriya. Tana bada gudunmawar da dama ga cibiyoyin raya al'umma domin rage wahalhalu da mata da yara ke fuskanta musamman a fanin kula da lafiya.

Tana daya daga cikin jagorori mata dake daga murya wajen kwato wa mata yancin su. Ko a makon da ya gabata ta yi kira ga mata wajen fitowa takara a zaben da za'a gudanar nan gaba.

Ta bada shawarar ne yayin da ta karbi bakoncin jaga-jigan mata na jam'iyar APC a fadar shugaban kasa makon da ya gabata.

No comments:

Post a Comment