Atiku Abubakar: Tsohon mataimakin shugaban kasa yace wa'adi daya zai yi idan aka zabe shi

I will rule for only one term - Atiku Abubakar

Atiku yace a shirye yake ya rattaba hannu ga takardar na tabbatar da cewa bai ketara alkawarin da ya dauka game da wa'adin sa.

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa a zaben 2019 Alhaji Atiku Abubakar yace wa'adi daya zai yi idan ya haye kujerar mulki.

Hirar shi da jaridar Thisday, dan takarar jam'iyar PDP ya sha alwashin tsaya kan batan shi na yin wa'adi daya a saman mulki.

Atiku yace a shirye yake ya rattaba hannu ga takardar na tabbatar da cewa bai ketara alkawarin da ya dauka game da wa'adin sa.

Ya kalubalanci shugaba Muhammadu Buhari idan yace shima ya dauki irin alkawarin a shekarar 2011 amma kuma ya saba wa alkawarin da ya dauka.

Yace alkawarin ta sha bam-bam da wanda Buhari dauka domin a shirye yake ya sa hannu ga takarda na tabbatar da yin wa'adi daya.

A kwannan  baya tsohon mataimakin shugaban kasa ya sha alwashin kawo karshen ta'adancin boko haran idan ya ci zaben 2019.

Ya fadi hakan ne a wajen taron jam'iyar PDP da aka gudanar jihar Borno cikin watan Juli.

No comments:

Post a Comment