Cinikin yan wasa: Chelsea tayi sabon gola, Courtois ya koma Real madrid

Sabon golan Chelsea Kepa Arrizabalaga

Kepa Arrizabalaga da Mateo Kovacic sun koma Chelsea yayin da tsohon golan Chelsea, Thibaut Courtois ya koma kungiyar Real Madrid.

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta karya asusun ta wajen siyan tsohon mai tsaron gidan Athletico bilbao Kepa Arrizabalaga.

Ta siye shi a kan fam miliyan 71 wanda da hakan golan ya kasance dan wasa mai tsaron gida mafi tsada a kasuwar cinikin yan wasa na wannan shekara.

Golan dan shekara 23 ya amince da yarjejeniyar da zai kai shi tsawon shekaru bakwai tare da Chelsea.

A wani bangare kuma tsohon golan kungiyar,Thibaut Courtois, ya koma Real Madrid. Zakarun turai sun siye shi ne a kan farashin fam miliyan 31. Dan kasar Belgium ya koma Madrid bisa ga kwangilar da zai sa ya shafe shekaru 6 a kungiyar.

Yarjejeniyar da Chelsea tayi da Real madrid ta amince da komawan dan wasan tsakiya Mateo Kovacic kungiyar Chelsea kan matakin aro har karshen kakar bana.

Tuni dai kungiyoyin suka kaddamar da sabbin yan wasan a farfajiyar su a shafukan sada zumunta.

Kasuwar cinikin yan wasa na cigaba da ci gabanin kulle ta yammacin ranar alhamis. Har yanzu kungiyoyi na rububi domin siyan dan wasa gabanin kararawar kasuwar tayi kara.

No comments:

Post a Comment