Dandalin kannywood: Rahama Sadau ta fitar da sabon kayan kwalliya da kamfaninta ta kera

Tauraruwar ta sanar da ranar fitar da man shafawan lebe tare da yin godiya ga yan uwa da abokanan huldar ta da suka taimaka wajen ganin ancinma manufar fitar da ita.

Fitacciyar jarumar dandalin wasan kwaikwayo ta masana'antar Kannywood Rahama Sadau ta shirya fitar da sabon kayan kwalliya ta man shafawa na lebe da ta kirkiro.

Jarumar bata sakaci wajen harkar kasuwanci musamman a bangaren harkar kwalliya, da wannan sabon jan baki da zata fitar, alamu na nuna cewa ta shirya damawa da sauran yan kasuwa a harkar kasuwanci.

Za'a fitar da sabuwar man mai suna Sadau matte liquid listick zuwa ga kasuwa ranar 14 ga watan Agusta.

 

Tauraruwar ta sanar da haka cikin farin ciki a shafin ta na dandalin sadarwa tare da yin godiya bisa irin gudunmawar da iyalen ta da sauran yan'uwa da abokanan aikin ta suka bada wajen ganin an cinma manufar fitar da man.

Kamar yadda ta sanar za'a fara siyar da kayan kwalliyan ne a kan farashin naira dubu biyu da dari biyar (2500).

Jarumar bata sakaci wajen harkar kasuwanci musamman a bangaren harkar kayan adon mata, da wannan sabon jan baki da zata fitar, alamu na nuna cewa ta shirya damawa da sauran yan kasuwa a harkar kasuwanci.

Sanin kowa ne cewa jaruma bata dogara da harkar fim wajen samun kudin shiga, tana da gidan kwalliyar mata mai suna Sadau beauty center kuma ga dukkanin alamu wannan sabuwar kayan kwalliyar zata zama fuskar gidan kwaliyar. Banda wanna akwai kuma Sadau pictures, kamfani mai daukar nauyin shirye-shiryen fim da makamantar haka.

Cikin wasa jarumar ta sanar cewa wata kila nan gaba za'a samu kamfanin "Sadau hotels".

Lamarin dai ya jawo farin ciki ga zukatan masoyan ta da sauran abokan aikin ta na dandalin kannywood.

 

No comments:

Post a Comment