Godswill Akpabio: Tsohon gwamnan Akwa Ibom ya sauya sheka zuwa APC

Dandazon jama'a sun halarcin babban taron bikin kaddamar da tsohon gwamnan jihar Akwa ibom zuwa jam'iyar APC a garin Ikot ekpene.

Shima tsohin gwmnan jihar Akwa ibom Godswill Akpabio ya shigo sahun manyan yan siyasan Nijeriya da suka sauya sheka daga wata jam'iya.

An gudanar da taron kaddamar dashi karkashin inuwar jam'iyar APC ranar laraba 8 ga watan Agusta. Dandazon jama'a sun halarcin babban taron kaddamar da dan majalisar dattawa jam'iyar APC a garin Ikot ekpene.

Tsohon shugaban jam'iya mai karancin rinjaye na majalisar ya koma jam'iya mai mulki tare da wasu yan majalisa hudu da kwamishnonin jihar Akwa ibom biyu da dimbi, magoya bayan sa.

A jawabin san wajen taron biki, Sanata Akpabio yace ya koma APC ne bayan ya gano cewa shugaba Muhammadu Buhari mutum ne mai adalci kuma mai kishin samad da cigaba a kasa.

Ya kuma ce dalilin dawowar shi jam'iyar shine domin kawar da talauci da yakar rashin adalci a kasa.

Dan majalisar ,mai shekaru 55 yace ya shigo inuwar APC ne domin taimaka wajen samad da cigaba a Nijeriya. A bayanin sa. Yace ya bar jam'iyar adawa ta PDP saboda rashin shugabanni na kwarai da kuma rashin kwakkwarar hangen nesa.

 

Daga karshe Sanatan yace zamanin mulkin PDP ta kare a yankin Nger-delta ya kare domin APC zata haye.

Bikin da aka shirya ta samu hallacin manyan jiga-jigan jam'iyar APC ciki har da shugaban jam'iyar Adams Oshiomole da Bola Ahmed Tinubu da sauran manyan yan siyasa da.

No comments:

Post a Comment