Hajj 2018: Hotuna daga hawan arafa


Ga wasu hotuna inda mahajjata ke hawan dutsen arafa domin sauke aikin hajj na wannan shekarar.

Sama da mahajjata miliyan biyu suka garzaya filin arafa daga Mina domin hawan dutsen Arafa duk a cikin ayyukan ibada da mahajjata ke gudanarwa.

Bana dai ranar hawan arafa ta fada ranar litinin 20 ga watan Agusta.

Masallacin da ake budewa sau daya ko wani shekara

A nan filin arafa mahajjata zasu gudanar da sallar azahar da la'asar a nan masallacin Nimra wanda ake budewa sau daya a shekara.

A nan masallacin Manzon Allah (SAW) ya gabatar da hudubar sa ta karshe. Ko wace ranar 9 ga watan Zul hijja nan masallcin ake gudanar da hudubar ake gudanar da hudubar aikin hajji.
Sai dai yana da matukar wahala mahajjata su je masallacin saboda wahakar cinkoso.

No comments:

Post a Comment