Hajj 2018: Yadda ake sauya rigar Ka'aba


Launin rigar baki ne kuma tana dauke da ratsin gwal mai nauyin kilogram 120 da kuma zaren azirfa.

A ko wace ranar 9 ga watan zul hijja na ko wani shekara ake gudanar da bikin sauya rigar dakin Ka'aba dake makka.

A duk shekara ake sabonta rigar daidai ranar hawan arafa.
Bikin wanda aka fi sani da Kiswah a larabci ta fada a dai-dai ranar litinin 20 ga watan Agusta.
Launin rigar baki ne kuma tana dauke da ratsin gwal mai nauyin kilogram 120 da kuma zaren azurfa.
Bikin sauya rigar na wannan shekarar ya biyo bayan guguwar iska da aka yi a Makka wanda ya  yaye barin rigar Ka'aba.
Kamar yadda aka wallafa a shafukan sada zumunta anyi  iska da ruwan sama a Makkah da Arafat da Mina da kuma Muzdalifah.

No comments:

Post a Comment