Labarai a takaice: Abubuwa 5 da suka faru a makon da ya shude

Nigeria's week in pictures: Here are the events that shaped Nigeria from August 6-10, 2018

Ga wasu muhimman abubuwan da suka faru a Nijeriya makon da ya gabata.

Ga wasu muhimman abubuwa da suka faru a  Nijeriya makon da ya gabata.

Hargitsi a zauren majalisar tarayya

Safiyar ranar Talata 7 ga watan Agusta jami'an rundunar fararen hula ta DSS suka yi ma zauren majalisar dokokin tarayya zagaye inda suka hana shiga da fita. lamarin dai ya jawo cece-kuce a fadin kasa inda wasu ke zargin cewa hakan ya faru duk a cikin shirin tsige shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki wanda ya sauya sheka daga APC zuwa PDP.

 

Hargitsin ya haddasa bacin rai inda wasu yan majalisar suka yi fito-na-fito da jami'an hukumar DSS da suka tare hanyoyin shiga.

Kawanya da jami'an suka yi ya biyo bayan ganawar da wasu sanatocin APC suka yi shugaban DSS tsakar daren ranar Litinin.

An sallami shugaban hukumar DSS, Lawal Daura

Sakamakon lamarin da ya faru a zauren majalisar dokoki, mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya sallami shugaban hukumar DSS Lawal Daura. Hakan ya biyo bayan ganawan da yayi da shugaban tare da sauran shuwagabanin hukumomin tsaroa a fadar shugaban kasa.

An kama Lawal Daura bisa wasu zargi da ake masa na daukar mataki ba tare da samun umarni ba. Har yanzu ana bincike kan batun sa.

An kuma nada Mathew Saiyefa a matsayin wanda zai maye gurbin sa a hukumar kasancewa shine ma'aikaci mafi matsayi a hukumar.

Mataimakin gwamnan Kano yayi murabus, ya koma jam'iyar PDP

Yayin da yan siyaya ke sauya sheka zuwa jam'iyun adawa, shima mataimakin gwamnan jihar Kano Farfesa Hafiz Abubakar ya dauki matakin sauka daga matsayin shi tare da sauya jam'iya zuwa PDP.

 

Tsohon mataimakin gwamnan ya yanke shawarar yin murabus daga kujerar shi bayan rashin jituwa da ya samu da gwaman jihar.

Babban na hannun daman tsohon gwamnan jihar sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya koma  jam'iyar da uban gidan sa yake ranar talata 7 ga watan Agusta.

Hirar shi da manema labarai bayan taron bikin komawar sa PDP, Farfesa Hafiz yace ya zama dole ya bar jam'iyar APC saboda irin azabtarwa da ya sha a cikin ta cikin yan shekaru da suka gabata.

Yace hakika zai samu sukuni a cikin sabuwar jam'iyar da ya koma tare da jaddada cewa har yanzu biyayyan da yake ma Kwankwaso tana nan kuma zai cigaba da goyon bayan sa a harkar siyasa.

Tsohon gwamnan jihar Akwa ibom ya sauya sheka zuwa APC

Tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom kuma shugaban jam'iya mai karancin rinjaye a majalisar dattawa Godswill Akpabio ya fice daga babban jam'iyar adawa ta PDP zuwa jam'iya mai Mulki ta APC.

An gudanar da taron kaddamar dashi a garin Ikot Ekene dake nan jihar Akwa Ibom wanda ya samu halarcin daruruwan jama'a tare da shugabanin jam'iyar APC.

A jawabin san wajen taron biki, Sanata Akpabio yace ya koma APC ne bayan ya gano cewa shugaba Muhammadu Buhari mutum ne mai adalci kuma mai kishin samad da cigaba a kasa.

Dan majalisar ,mai shekaru 55 yace ya shigo inuwar APC ne domin taimaka wajen samad da cigaba a Nijeriya. A bayanin sa. Yace ya bar jam'iyar adawa ta PDP saboda rashin shugabanni na kwarai da kuma rashin kwakkwarar hangen nesa.

Ahmed Musa ya samu kyakkyawar tarba a sabon kungiyar shi na kasar Saudiya

Gabanin karshen makon, dan wasa mai tauraro Ahmed Musa ya gamu da kyakkyawar tarba a kasar Saudi Arabia yayin da ya koma sabon kungiyar sa ta Al-nassr.

 

Dandazon masoyan dan wasa da kungiyar suka fito domin yi masa maraba yayin da ya sauka filin jirginm sama na King Faisal dake nan garin Riyadh.

No comments:

Post a Comment