Maryam Sanda: Wanda ake zargi ta kashe mijinta ta haifar masa yaro

Maryam Sanda with her late husband, Bilyamin Bello when the going was good

Kamar yadda labari ya bayyanar za'ayi bikin sunan jaririn ranar 14 ga watan Agusta.

Maryam Sanda wanda ake tuhuma da zargin kashe mijinta ta haifar masa da yaro kuma ana shirin yin bikin suna nana bada dadewa.

A labarin da Sahara reporters ta fitar, Maryam ta haifi jinjirin ne a makon da ya gabata inda kuma za'ayi bikin sunan jaririn ranar 14 ga watan Agusta. Sai dai za'a gudanar da bikin sunan yaro ne cikin sirri kamar yadda rahoton ya bayyana.

Tana fuskantar tuhuma a kotu kan zargin kashe mijinta Bilyamin Bello dan-dan tsohon shugaban jam'iyar PDP a shekarar 2017 a gidan su dake nan Wuse 2 na garin Abuja.

An tabbatar da rasuwar sa a asibiti bayan da aka ruga dashi domin ceto rayuwar shi bayan da aka caka masa kwalba.

Maryam ta samu rangwami a kotu bisa juna biyu da take dauke dashi. Kotu ta bata damar yin beli daga gidan kaso sakamakon cikin da take dauke dashi.

Maryam Sanda wanda diyyar tsohuwar mai ruwa da tsaki na bankin Aso Savings ce ta kashe mijin ta Bilyaminu bisa ga zargin cewa yana nema ya kara aure.

Anyi kokarin samar da beli tun lokacin da lamarin ya faru kasancewa tana tare da jaririya yar wata shidda wanda take shayarwa. Kotu ta bata damar yin beli cikin watan Maris na bana bayan da ta gano cewa tana dauke da ciki.

No comments:

Post a Comment