Ta'adanci boko haram: Sojoji dake yakar yan ta'adda sunyi bore a filin jirgin saman Maiduguri

Sojojin sun shafe kusan sa'o'i hudu suna harbi sama tare da yin barazana ga kwamandojinsu.

Ranar Lahadi da misali karfe 6;30 na yamma wasu sojoji dake rundunar operation lafiya dole masu yaki da mayakan boko haram suka yi bore a filin jirgin sama dake Maiduguri.

Kamar yadda rahotanni suka bayyana, sojojin sun nuna bacin ran su ne bisa umarni da aka basu na komawa fagen daga na garin Marte sabanin Maiduguri inda suke.

A rahoton da kamfanin dillanci labarai ta Reuters ta ruwaito, sojojin sun shafe kusan sa'o'i hudu suna harbi sama tare da yin barazana ga kwamandojinsu.

Daya daga cikin fusatattun sojojin yana mai furta cewa "Muna jin haushi shi yasa muke harbi. Don maye za'a mayar damu fagen daga bayan shafe shakaru hudu ana damawa"?

Sojojin suna masu ikirari cewa shekara uku aka sanar masu cewa zasu yi suna yakar yan ta'adda.

Lamarin dai ya faru yayin da tawaga ta biyu na alhazan jihar ke shirin tashi zuwa kasa mai tsarki.

Hukumar dake kula da lamuran filin jirgin sama FAAN tace aika-aikar sojojin bata haddasa wata matsala ba wanda tayi sanadin dakile ayyukan filin.

An shawo kan lamarin

Sakamkon abun da ya faru, rundunar Operation lafiya dole tace an shawo kan sojojin kuma kura ta lafa.

A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun kakakin rundunar, Kanal Onyema Nwachukwu, shugaban rundunar ya shiga tsakani kuma yayi masu bayani wanda har suka gamsu da ita.

Sai dai sanarwar ta kara da cewa  za a dauki mataki, domin tabbatar da cewa hakan bai sake faruwa ba.

Sojojin suna iya fuskantar ladabtarwa domin dokar sojoji ta hana yin bore da bijire ma doka.

No comments:

Post a Comment