Ahmed Musa ya sake birge jama'a, ya zura kwallo uku a raga

Wasan su da kungiyar Al-Qadisiyah wanda aka tashi 3-0 Ahmed Musa nasarar saka dukanin kwallayen a radar abokan adawar su.

Tauraron fitaccen dan wasan super eagles ta Nijeriya wato Ahmed Musa tana cigaba da haskawa a sabon kungiyar shi dake kasar Saudi Arabia.

Dan wasan ya ceci kungiyar sa Al-nassr a wasan da suka buga da abokan adawar su na gasar firemiya na Saudiya inda shi kadai ya zura kwallaye uku da suka taimaka wajen samun galaba.
Wasan su da kungiyar Al-Qadisiyah wanda aka tashi 3-0 Ahmed Musa nasarar saka dukanin kwallayen a radar abokan adawar su.

Dan wasan mai shekaru 25 yayi nasarar saka kwallayen ne a cikin mintuna 20 da 40 da 66 na wasan wanda aka buga daren ranar Laraba.
Sakamakon wasan ya taimakin kungiyar wajen zama na farko a teburin gasar.
Al-Nassr ta sau maki 9 sakamakon zarran da tayi bayan wasanni uku na gasar da ta buga.

Ahmed Musa bai gaza nuna farin cikin sa bisa wannan nasarar da ya samu na zurra kwallaye uku a wasa daya.
Dan wasan ya saka wani faifan bidiyo mai nuna yadda ya saka kwalla daya daga wasan a shafin sa na kafafen sada zumunta.


No comments:

Post a Comment