An gano wata kabila a Najeriya da har yanzu ke sayar da ‘ya’ya mataA zamanin baya kafin zuwan addinai da wayewar kai, ana daukan haihuwar diya mace tamkar wata annoba.
Amma abun mamaki, sai ga shi an samu wata kabila da ake kira Becheve, a Najeriya, da har yanzu suke cinikayya da ‘ya’ya mata - A kabilar ta Becheve, uba kan siyar da diyarsa mace ko kuma ya bayar da ita a matsayin biyan bashi ga mutumin dake binsa bashi An samu wata kabila da ake kira “Becheve” a karamar hukumar Obanliku dake jihar Kuros Riba a kudancin Najeriya da har yanzu suke sayar da ‘ya’ya mata ko musayarsu domin biyan bashi. Kabilar Becheve tayi suna a jihar Kuros Riba wajen yiwa ‘ya’ya mata dake da karancin shekaru auren dole. 

No comments:

Post a Comment