An saki malaman makarantar Shehu Idris da aka sace A zaria

Barayin sun savci malaman ne ranar Lahadi 16 ga wata a daidai lokacin da suke hanyar su na komawa makarantar daga Zaria.

Labari mai dadi ya fito cewa barayin da suka sace malaman uku na makarantar koyon aikin kiwon lafiya ta Shehu idris dake Makarfi sun sake su.

Malam Yusuf Yakubu wanda ke kula da alamuran makarantar ya tabbatar da haka ranar Talata 18 ga watan Satumba.
A labarin da jaridar Dailytrust ta fitar an saki malaman ne bayan kwana biyu da sace su.
Yakubu ya shaida cewa an saki malaman ne a dai dai karfe 8:00 na daren ranar Talata.
Kamar yadda ya bayyana masu garkuwan sun saki malaman ne bayan yarjejeniyar da makarantar tayi da su.
Sai dai bai bayyana ainihin matakin da suka dauka gabanin sakin su.
Barayin sun savci malaman ne ranar Lahadi 16 ga wata a daidai lokacin da suke hanyar su na komawa makarantar daga Zaria.
Malaman da aka sace sun hada da  Dr Akawu, da Halima Mallam da Rabi Dogo.

No comments:

Post a Comment