Gasar Fifa best: An fitar da yan wasa uku da zasu fafata wajen zama gwarzon duniya, Messi baya ciki


Bayan shafe tsawon shekaru 11 yana daya daga cikin yan wasa uku da suke karawa wajen zama gwarzon shekara, bana Messi baya cikin lissafi.

Hukumar kwallon kafab ta duniya FIFA ta fitar da sunayen yan wasan uku da zasu fafata wajen lashe kyautar gwarzon shekara. Gwarzon dan wasan kungiyar Barcelona kuma wanda ya lashe kyautar sau 5 baya cikin yan wasa uku da akar fitar.

Wannan shine karo na farko cikin shekaru 11 da Messi ya gaza shiga cikin jerin yan takara uku wajen lashe kyautar.
Kamar yadda hukumar ta fitar ranar litinin 3 ga watan Satumba yan wasa uku da zasu fafata wajen lashe lambar yabo na wannan shekarar sun hada da tsohon abokin hamayyar Messi wato Cristiano Ronaldo da Luka Modric na kungiyar Real Madrid da dan wasan kungiyar Liverpool, Mohammed Salah.
Daya daga cikin su zai lashe kyautar zama gwarzon shekara bisa rawar da ya taka a filin kwallo.
Tauraron dan wasan Real Madrid zai nemi ya lashe kyautar bayan yayi nasarar zama gwarzon nahiyar turai kwanan baya.
A bangaren takarar gwarzon kociya, kocin zakarun kofin duniya Faransa, Didier Deschamp zai fafata da tsohon kocin Real madrid Zinedine Zidane da kocin kasar Croatia Zlatko Dalic wajen lashe kyautar gwarzon kociya.
Hakazalika Hugo Loris na kasar Faransa da kungiyar  Tottenham zai kara da Kasper Schmechel na kasar Denmark da kungiyar Leicester tare da Thibout Courtois na kungiyar Real madrid wajen zama gwarzon mai tsaron gida na gasar.
A bangaren mata kuwa tauraruwar kasar Brazil, Marta, wanda tayi nasarar lashe kyautar sau biyar zata sake fafata wajen lashe kyuatar tare da yar wasar kasar Norway da kungiyar Lyon Ada Hegerberg da kuma Dzsenifer Marozsan na kasar Jamus.

No comments:

Post a Comment