Gwamna Ganduje ya rantsar da sabon mataimakin sa

Anyi bikin rantsuwar ne a babban dakin taro na gidan gwamnatin jihar Kano ranar Laraba 19 ga watan Satumba.

Kwana  biyu bayan amincewar majalisar jiha, Gwamnan jihar Kano Abdullahi umar Ganduje ya rantsar da sabon mataimakin sa.

Majalisar ta amince dashi a zaman da tayi ranar Talata bayan da dan majalisa Zubairu Masu ya shigar da kuddurin tabbatar dashi a farfajiyar majalisar wanda Kabiru Rurum ke jagoranta.
Anyi bikin rantsuwar ne a babban dakin taro na gidan gwamnatin jihar Kano ranar Laraba 19 ga watan Satumba.
Dr Nasiru Yusuf Gawuna ya maye gurbin tsohon mataimakin gwamnan wanda yayi murabus cikin watan Agusta.
Tsohon mataimakin gwamnan ya dauki matakin ajiye mukamin sa a gwamnatin jihar bisa wasu dalilai na rashin jituwa tsakanin sa da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje.
Gabanin wannan mukamin, tsohon kwamishnan ya taba zama shugaban karamar hukuma kana ya rike mukamin shugaban hukumar wasanni ta matasa na tarayya.

No comments:

Post a Comment