Gwamnatin India Ta haramta Saki Uku

Biyo bayan kin amincewar majalisar zartaswa na wannan kuduri, ya sa gwamnatin kasar ta India ta yi amfani da karfin ikon da kundin mulkin kasar ya bata, wajen tabbar da kudurin ya zama doka, dokar ta gwamnatim ta ce zata fara aiki ba bata lokaci ba.
Daga cikin abubuwan da dokar ta kunsa, akwai hukuncin daurin shekaru 3 ga duk wani musulmi da aka kama da laifin yiwa matarsa saki uku a lokaci daya, tare da biyan tara. A farkon shekara ta 2017, Fira Ministan India Narendra Modi, ya baiwa mata kariya kan hakkokinsu na aure ta hanyar bullo da wani sabon kuduri, sai dai shima wannam kudurin ya sha ruwa a gaban majalisar, bayan gaza samun rinjaye a amincewar yan majalisar.

No comments:

Post a Comment