Gwamnatin Nigeria ta datakar da ranar kaddamar da jirgin sama

Sanarwar haka a fito ne daga ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika ta hanyar wani sako da ya wallafa a shafin sa na Tuwita.

Gwamnatin tarayya ta dakatar da shirin ta na kafa sabon kamfanin jirgin saman "Nigeria Air" watanni kadan kafin ainihin lokacin da aka kayyade domin fara aikin jiragen.

A cikin watan Yuli na bana babban ministan sufurin jirgin sama ya sanar da cewa kamfanin zata fara aiki cikin watan Disamba.
Wannan sabon matakin da gwamnatin tarayya ta dauka game da batun ya biyo ne bayan zaman majalisar da aka yi ranar Laraba kamar yadda aka saba yi a mako-mako.
Sanarwar haka a fito ne daga ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika ta hanyar wani sako da ya wallafa a shafin sa na Tuwita.
Ministan yace majalisar ta jinkirta aikin kafa kamfanin jirgin saman na wucin-gadi.
Sai dai ministan bai bayyana ranar da za'a cigaba da aikin kamfanin har i'zuwa ranar da jiragen zasu fara ketara hazo.

No comments:

Post a Comment