Maryam Booth ta samu babban matsayi a gidauniyar Atiku

Maryam Booth ta shiga sahun sauran abokan aikin ta na masana'antar kannywood dake rike da matsayi karkashin wannan gaidauniyar.

Fitacciyar jaruma Maryam Booth ta samu babban matsayi a gidauniyar tsohon mataikin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar.

Gidauniyar Atiku Care Foundation wacce take tallafa wa mara sa galihu ta daukaka mukamin ta daga jakadiya zuwa mukamin mataimakin shugaba na  yankin arewa.
Gidauniyar ta sanar da hakan ne ta  hanyar wani sako da ta wallafa a shafin ta na kafafen sadarwa inda ta bayyana cewa matsayin zai fara aiki daga ranar juma'a 21 ga watan Satumba.
Maryam Booth ta shiga sahun sauran abokan aikin ta na masana'antar kannywood dake karkashin wannan gaidauniyar.
Wasu daga cikin fitattun jarumai da suka samu matsayi a gidauniyar sun hada da Fati MuhammadRashida Adamu da Abdu Boda.
An kafa gidauniyar ne domin taimakawa mara hali tare da nuna aikin tallafawa da Atiku Abubakarkeyi ga idon jama'ar Nijeriya har da na kasashen waje.
Har ila yau gidauniyar Atiku Care Foundation ta zama cibiya da tsohon mataimakin shugaban kasa ke samu yana mu'amala da yan kasa a ko wani lungu da sako ta hanyar kafafen sadarwa da gidauniyar ta kafa.

No comments:

Post a Comment