Masu garkuwa da mutane sun sace dan shugaban jam'iyar APC na Borno

Kwamishnan yan sanda na jihar Borno Mista Dermian Chukwu ya tabbatar da faruwar haka yayin da ya zanta da manema labarai a garin Maiduguri.

Masu garkuwa da mutane sunyi awon gaba da dan dan, Alhaji Ali Bukar-Dalori shugaban jam'iyar APC reshin jihar Borno.

Barayin sun sace dan mai shekara hudu a duniya a makarantar sa ta Maiduguri Capital Schoolranar Laraba 19 ga watan Satumba.
Kwamishnan yan sanda na jihar Borno Mista Dermian Chukwu ya tabbatar da faruwar haka yayin da ya zanta da manema labarai a garin Maiduguri.
Yace barayin sun sace jaririn a makarantar sa kuma sun garzaya dashi maboyar su.
Kwamishnan ya kara da cewa an kaddamar da dakaru na musamman domin kubutar da jaririn.
Daga karshe yayi kira da babban murya ga yan siyasa da su kaurace yin bita-da-kulli ga sauran abokan adawar su domin cinma wani manufa na siyasa.
Haka zalika yayi kira ga iyaye da su lura da ya'yan su kana suyi maza-maza su shigar da kara wurin jami'an tsaro idan suka lura

No comments:

Post a Comment