Rikicin jam'iyar PDP a Kano: Mallam Ibrahim Shekarau ya fita daga PDP


Ya ce ya fice ne daga jam'iyyar saboda zargin rashin adalci a bangaren shugabannin jam'iyyar na kasa wajen rushe shugabancin jam'iyyar na jihar Kano, da yunkurin mikawa Kwankwaso shugabancin.

Tsohon gwamnan  jihar Kano kuma dan takarar shugaban kasa Malam Ibrahim Shekarau ya fice daga  PDP.


Tsohon gwamnan wanda yayi mulkin jihar Kano na Tsawon shekaru 8 ya fice daga babban jam'iyar adawa ta PDP safiyar ranar talata kamar yadda mai magana da yawun sa Sule Ya'u Sule ya sanar.
Hirar shi da gidan rediyo ta Freedom FM, hadimin tsohon gwamnan ya sanar cewa Shekarau ya fice daga PDP sakamakon rusa jagororin jam'iyar a jiha da uwar jam'iya tayi.
Ya ce ya fice ne daga jam'iyyar saboda zargin rashin adalci a bangaren shugabannin jam'iyyar na kasa wajen rushe shugabancin jam'iyyar na jihar Kano, da yunkurin mikawa Kwankwaso shugabancin.
Ya kara da cewa gabanin daukar matakin fita daga PDP sai da ya zauna da shugabancin jam'iyar domin gabatar da korafinsu da kuma kokarin warware matsala da jam'iyar ke fuskanta a jihar.
A ranar Asabar din da ta gabata ne uwar jam'iyyar PDP ta kasa ta bayar da sanarwar rushe shugabancin jam'iyyar na Kano, sai dai har yanzu ba a bada dalilan daukar matakin ba.
Kamar yadda Sule Yau ya sanar cewa a sanarwar da mai magana da yawun jam'iyyar ya fitar ta ce za a maye gurbin shugabannin da aka rushe da kwamitin rikon kwarya.
Jiya ranar litinin 3 ga watan Satumba wasu dubban yan PDP suka gudanar da zanga-zangar adawa bisa ga matakin da uwar jam'iyar ta dauka.
Kai ga yanzu Shekarau bai bayyana jamíyar da zai koma shi da magoya bayan sa.
Sai dai wasu na hasashe cewa zai koma tsohon jam'iyar sa na APC wanda tare dashi aka gina ta.
Shekarau ya fice daga APC ne a cikin shekaran 2014 bayan zargin rashin adalci da yayi ma shuwagabanin jam'iyar na wannan lokacin ta hanyar fifita Kwankwaso a kansu.

No comments:

Post a Comment