Sojoji sun fatattaki yan ta'ada biyar a jihar Borno

Rundunar sojojin Nijeriya tace dakarun ta tayi nasarar fatattaki wasu mayakan Boko Haram yayin da suke kai-kawo a karamar hukumar Bama dake jihar Borno.

A sanarwar da kakakin rundunar Birgediya Janar Texas Chukwu ya fitar a garin Maiduguri, yace dakarun sunyi nasarar hakan ne a garuruwan Kote da Bula Dadobe na karamar hukumar.
Yace gamayyar dakarun 'Operation Rainbow' suka gudanar da aiki na musamman ranar asabar da Lahadi a yankin inda a nan suka gano shingen yan ta'adar.
Cikin makamai da aka gano tare dasu akwai bindiga kerar AK-47 guda uku da Bama-bama tare da na'urorin kirkirarta da babura biyu da kuma keke guda takwas.
Daga karshe kakakin yayi kira ga jama'a da su taimaka da cigaba da labari cikin lokaci da zai taimaki jami'an tsaro wajen cinma manufar su na tabbatar da tsaro.

No comments:

Post a Comment