Tsohon gwamna Jos JOSHUA DARIYE wanda ke Kulle gidan yari ya mika fom din tsayawa takarar sa

Dafat yace har yanzu Joshua Dariye na da farin jini duk da lamarin da yake fuskanta kuma akwai yiyuwar ya ci zaben fidda da gwani daga kurkuku.

Tsohon gwamnan jihar Filato wanda ke garkame a gidan kaso sakamakon laifin wawure kudin jama'a da aka kama shi da yi ya mika takardar tsayawa takarar sa.
Tsohon gwamnan yana fuskantar shekaru 14 a gidan yari sakamakon laifin da aka kama shi amma yana da burin sake tsayawa takarar a zaben 2019.

Kamar yadda jaridar Dailytrust ta fotar da rahoto mai magana da yawun jam'iyar APC ta jihar Filato Mista Chindo Dafat ya tabbatar da labarin haka.

Dafat yace tsohon gwamnan ya cike fom dinsa kuma ya mika ta ga jam'iyar inda kuma zai tsaya takarar fidda da gwani da sauran yan takarar uku dake neman kujerar dan majalisar dattawa wanda zai wakilci yankin Filato na tsakiya.

A cewar kakakin, sakataren mazabar tsohon gwamnan ya sa hannu ga takardar a madadin sa kuma dinbim magoya bayan sa na cigaba da yi masa kamfe.

Dafat yace har yanzu Joshua Dariye na da farin jini duk da lamarin da yake fuskanta kuma akwai yiyuwar ya ci zaben fidda da gwani daga kurkuku.

"banda nasarar da muke sa ran zai samu game da karar sa ya shigar kan laifin sa, muna cigaba da yi masa add'uar samun rangwami daga jiha" yace.

Duk da cewa uwar jam'iyar ta bayyana cewa babu yanda wanda ke garkame a gidan yari zai nemi takara domin doka bata bada dama ba, Dafat yace doka bata hana shi siyan fom din tsayawa takara.

A ciki wata takardar sanarwa da kakakin jam'iyar APC na kasa,Yekini Nebena, ya fitar ranar Talata 11 ga watan Satumba, jam'iyar tace baza da yarda tsohon gwamnan ya fito takara ba.

A cewar shi wannan ba shi bane karo na farko da wanda ke garkame a gidan yari zai tsaya takara. Ya bada misali da tsohon dan majalisar dattawa daga jihar Osun, Iyiola Omisore, wanda ya lashe zaben takarar majalisa duk da cewa yana gidan yari.

Lamarin takarar tsohon gwamnan ya janyo cece-kuce tsakanin jama'ar kasa.

Babban jam'iyar adawa ta PDP tace lamarin abun mamaki ne kuma akwai cin fuska domin doka bata goyi bayan yin haka.

Hukuncin daurin shekaru 14 a gidan yari
Joshua Dariye ya samu hukuncin ne bayan ga karar da hukumar hana cin hanci da rashawa ta EFCC ta shigar wanda take zargin shi da wawure kudin jama'a sanda yake gwamna.

A zaman kotu da aka yi ranar talata 12 ga wata, an kama Dariye da aikata laifufuka 15 daga cikin 23 da aka shigar a kansa.

Bayan ga haka an kuma kama shi da canza arkalar naira biliyan daya na daga cikin asusun gyara muhalli.

Kamar yadda aka bayyana a kotu, tsohon gwamnan wanda yake dan majalisar dattawa yanzu ya sauya manufar kudin ne ta hanyar wata kamfani mallakar shi mai suna Ebenezer Reitner Ventures.

Mai sharia Adebukola Banjoko ta zantar da hukunci bayan shafe sa'o'i 5 ana muhawara a kotu.

No comments:

Post a Comment