Yadda aka karrama gwarzayen kwallo kafa a gasar FIFA na 2018


Jarumin Hollywood, Idris Elba, ya jagoranci taron bikin bana wanda aka gudanar a birnin London ranar Litinin 24 ga watan Satumba.

Hukumar kwallon kafa ta duniya ta gudanar da bikin gasar karrama fitattun yan wasa da suka taka rawar gani a duniya kamar yadda ta saba a ko wani shekara.

An gudanar da bikin bana a dakin taro na London's Royal Festival Hall dake birnin London.
Bikin ya samu hakarcin manyan fuskoki a duniya kwallo, tsofaffi da na yanzu tare da manyan masu ruwa da tsaki a duniyar kwallo.
Shahararren jarumin fina-finan Hollywood na Amurka, Idris Elba, ya jagoranci taron bikin bana.
Dan wasan kungiyar Real Madrid da kasar Croatia, Luka Modric, shine ya zama gwarzon shekara.

Ya doke Cristiano Ronaldo da Mohamed Salah wajen lashe kyautar bisa ga gwaninta da ya nuna a kakar bana.
Mohammed Salah; ya lashe kyauta na zura kwallo mafi birgewa a raga na gasar bana.
Kocin Faransa, Didier Deschamp, ya lashe kyautar gwarzon koci na shekara.

Mai tsaron ragar Real da Belgium, Thibaut Courtois, shine gwarzon shekara a rukunin takarar gola na gasar.

A rukunin mata na gasar, yar wasan kasar Brazil, Marta, ya lashe kyautar gwarzuwar shekara.

Kociyar tawagar mata na kungiyar Olympique MarseileReynald Pedros, ita ce ta lashe kyautar kociyar shekara.
Tawagar yan wasan FIFA na wannan shekara sun hada da:

David De gea, Marcelo, Dani Alves, Sergio Ramos, Rapheal Varane,  Luka Modric, N'golo Kante, Eden Hazard, Lionel Messi, Kylian Mbappe, Cristiano Ronaldo.

1 comment: