Za'a buga wasan Nijeriya da Libya na gasar kofin Afrika a kasar Tunisiya

Libya zata karbi bakoncin Nijeriya a wajen gida sakamakon dakatarwa da hukumar FIFA ta ba kasar game buga wasa a kasar bisa ga dalilin rikicin siyasar dake faruwa a kasar.

Rahotanni na nuna cewa yan wasaEagle ta Nijeriya zasu garzaya kasar Tunisiya domin karawa da kasar Libya a wasan neman shiga gasar kofin Afrika.

Libya zata karbi bakoncin Nijeriya a wajen gida sakamakon dakatarwa da hukumar FIFA ta ba kasar game buga wasa a kasar bisa ga dalilin rikicin siyasar dake faruwa a kasar.
A da an sanar cewa za'a buga wasan a kasar Algeria bisa ga wannan sabon rahoton arkallar ta karkata zuwa Tunisiya.
Hukumar kwallon kafar Libya bata yi karin bayani game da wanan sabon sauyin da suka yi.
Tawagar yan wasan zasu kece raini da na kasar Libya cikin jerin wasanin neman shiga gasar kofin Afrika da za'a buga shekara mai zuwa.
Nijeriya zata buga wasan ta na uku na rukunin D da da kasar arewacin afrika ranar 10 ga watan Oktoba.
Wasan ta na farko Nijeriya ta fadi inda kasar Afrika ta kudu ta doke ta da ci biyu babu. Wasan ta na Biyu Nijeriya ta lallasa kasar Seychelles da ci uku babu ko daya.
Tawagar zasu nemi su tabbatar da matsayin su domin shiga gasar afrika da anniyar samun galaba akan Libya.
A halin yanzu Nijeriya ce na uku a rukunin D da maki uku yayin da Libya da Afrika ta kudu suka raba maki hudu hudu kuma suka zama na jagororin rukunin.

No comments:

Post a Comment