Ziyarar shugaban kasa: Kalli yadda yan kasar Sin suka nishadantar da shugaba Buhari a Beijing


Yan kasar sun nishadantar da shugaban yayin da ya gana da yan Nijeriya mazauna kasar a farfajiyar ofishin jakadan Nijeriya dake Beijing.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai ziyara kasar sin inda zai halarci taron Kasar Sin da Africa wanda za'a gudanar ranar 3 ga wata zuwa 4 ga wata.

Shugaban ya saukar birnin Beijing tare da tawagar majalisar sa tare da wasu gwamnoni sda sanotoci ranar asabar 1 ga wata.
Jim kadan bayan saukar sa shugaban ya gana da wasu yan Nijeriya mazaunin kasar Sin tare da da dalibai yan Nijeriya masu karatu a kasar.
A taron ne wasu yan kasar suka nishadantar da shugaban da wakae "Allah raini Baba" tare da kwaikwayar rawar wakar wanda mawakiya Ummi.

yan kasar sun nishadantar da tawagar shugaban da wakar wanda aka rera cikin harshen fulbe ko Fulatanci kamar yadda aka fi sani.

A cikin faifan bidiyo da hadimin shugaban ya wallafa a shafin sa na kafar sada zumunta an gan inda tawagar gwamnati kasar ke cike da al'nashuwa tare da jinjina ma matasan da suka nishadantar dasu.
Nijeriya zata yi kokari kulla kyakkyawar alaka da kasar Sin wajen farfado da harkar kasuwanci a kasar tare da kulla yarjejeniya da wasu manyan yan kasuwa wajen zuba jari a Nijeriya.

No comments:

Post a Comment