Dan Nijeriya Ya Lashe Gasar Cin Abinci Mai Mugun Yaji A Kasar Chana


Daga Mainasara Nasarawa Funtua

Wannan gasa mutane daga kasashe biyar ne suka shiga domin gwada sa’arsu ta cinye wani dandakakken nama mai dankaren yajin barkono.

Sai dai kuma dukkan wadanda suka shiga gasar sun gaza cinye abincin yayin da shi dan Nijeriya ya cinye ya kuma sude kwanon. 

An karrama dan Nijeriyar da ya ci gasar da lambar yabo.

No comments:

Post a Comment