Khadija Ibrahim: Minista ta doke danta wajen zama gwanin APC a jihar Yobe


Rahotanni daga jihar na nuna cewa duk da matsin lamba da jama'a suka yi masa na janye takarar sa ma matar mahaifin sa, Muhammed yaki amince da yin haka.

Karamar ministan harkokin kasashen waje, Hajiya Khadija Ibrahim, ta doke dan abokiyar zaman auren ta wajen zama gwanin APC na takarar wanda zai wakilci dundumar Damaturu/Gulani/Gujba/Tarmuwa a majalisar wakilai na tarayya.

Baturen zaben fidda gwani da jam'iyar APC ta gudanar a jihar, Farfesa Abba Gambo, ya kaddamar da ita a matsayin wacce ta lashe zaben takarar kujerar ranar Laraba 3 ga watan Oktoba.
A zaben aka gudanar, Hajiya Khadija ta samu kuri'u mafi rinjaye inda ta samu 1295 yayin da shi kuma danta, Muhammed Ibrahim, ya samu kuri'u 15.
Rahotanni daga jihar na nuna cewa duk da matsin lamba da jama'a suka yi masa na janye takarar sa ma matar mahaifin sa, Muhammed yaki amince da yin haka.
Kamar yadda muka samu labari, sauran yan takara biyu dake neman kujerar, Alhaji Abdullahi Kukuwa da Alhaji Ahmed Buba, sun janye takarar su domin baiwa ministan dama.
Ministan ta kuma yaba masu bisa halarcin da suka yi mata.
Uwargidan tsohon gwmnan jihar Yobe zata daga tutar APC a zaben 2019 a takarar majalisar wakilai na tarayya.

No comments:

Post a Comment