Kungiyar Madrid Za Ta Maye Gurbin Kociyanta Da Conte

Rahotonni sun nuna kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta shirya korar kociyanta, Julen Lopetegui don maye gurbinsa da Antonio Conte tsohon kociyan Chelsea da kungiyar Juventus, rade-radin korar Lopetegui ta yi kamari ne bayan da babbar kungiyar adawa ta Barcelona, ta lallasa kungiyar Madrid din da ci 5 da 1 a jiya Lahadi.
Lopetegui din wasan hudu kadai ya ci ma Madrid, inda ya yi kunnen doki biyu, sannan aka sha su a wasanni hudu, a halin yanzu kungiyar ta Madrid tana ta tara a jerin kungiyoyi a gasar La Liga ta bana. Lopetegui mai shekaru 52, kungiyar kwallon kafa ta kasar Spaniya ta kore shi gab da za a fara wasannin gasar cin kofin duniya da a kammala a kasar Rasha, bayan da ya sanya kwantiragi da kungiyar ta Madrid.
Wasu suna ganin ba laifin Lopetegui bane halin da kungiyar Madrid din ta shiga, sai dai ya zama tafiyar zakaran dan kwallon kungiyar wai da sauya sheka zuwa kungiyar Juventus, Ronaldo shi kai yana iya sha wa kungiyar Madrid kwallaye 50 a kakar wasa.
Ana ganin ranar Asabar mai zuwa Conte zai karbe horar da kungiyar Madrid, inda kungiyar za ta kara da kungiyar Valladolid a wasan La Liga.

No comments:

Post a Comment