Mourinho Ya Na Kan Hanyar Koma Wa Real Madrid

Tsohon shugaban gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Ramon Calderon ya bayyana cewa yana ganin nan gaba kadan tsohon kociyan kungiyar Jose Mourinho zai koma Real Madrid.
Calderon yayi wannan bayani ne a wata hira da yayi da manema labarai inda yace ko kusa ko nesa tabbas Mourinho zai koma Real Madrid saboda a irin wanann lokaci kungiyar tana bukatar mai koyarwa kamarsa.
Mourinho dai yana cikin wani mawuyacin hali a kungiyar Manchester United sakamakon rashin kokarin da kungiyar tafara dashi a gasar firimiya sannan kuma itama Real Madrid tana fama da rashin nasara kuma zata iya korar kociyan nata.
“Indai shugaban gudanarwar kungiyar yana kungiyar nanda wasu ‘yan lokuta tabbas Mourinho yana kan hanyar komawa Real Madrid kuma lamarin zai iya faruwa nan kusa” in ji Calderon Ya ci gaba da cewa “Babu wani mai koyarwa da Flortentino yake girmamawa a duniya kamar Mourinho duk da cewa yabar kungiyar kuma sunada alaka mai girma da karfi a tsakaninsu”
A yau Real Madrid zata fafata wasan hamayya da kungiyar kwallon kafa ta Barcelona yayinda itama Manchester United zata fafata wasa da kungiyar kwallon kafa ta Eberton a filin wasa na Old Trafford.

No comments:

Post a Comment