Mutane Shida Daga Cikin Wadanda Ake Nema Ruwa A Jallo Sun Shiga Hannu

KISAN JANAR ALKALI

Mutane Shida Daga Cikin Wadanda Ake Nema Ruwa A Jallo Sun Shiga Hannu

Zuwa yanzu mutum 6 cikin wadanda rundinar ‘yan sandan Nigeria reshen jihar Pilato take nemansu ruwa a jallo bisa zargin hallaka Janar Idris Alkali sun shiga hannu, kuma ana cigaba da tuhumarsu.

A tuhumarsu da ake bincike ya nuna cewa wannan da kuke gani a hoto Timothy Chuan direban tifa ne, shine wanda ya tuka motar Janar Idris Alkali daga inda suka hallakashi har zuwa bakin kududdufin da suke jefa motar.

Timothy Chuwan yana daga cikin wadanda suka tare motar Janar Idris Alkali kamar dai yadda ‘yan fashi da makami suke tare matafiya, bayan Janar Idris ya gabatar da kansa cewa shi General ne a gidan soji, amma basuji tsoro ba suka kamashi suka hallakashi nan take, suka raba kayan sakawansa suka raba kudinsa da wayoyinsa, shi kuma Timothy Chuan ya toka motar Janar din ya kai kududdufin Dura-Du.

Tun daga yanzu garin Dura-Du ya fara komawa kufayi, ance duk sun tsere sun gudu daga gidajensu, duk da sojoji basu taba kowa ba a garin bincike suke, amma har sun gudu shaguna da gidajensu duk a kulle sun bar gonakinsu da dabbobinsu, basu ga komai ba tukunna sai an samo gawar Janar.

Allah muna rokonKa Ka saukar da bala’i akan dukkan wadanda suke da hannu da wadanda suka boye gaskiya game da kisan Janar Idris Alkali.

No comments:

Post a Comment