SANARWA GAME DA BACEWAR JANAR IDRIS ALKALISANARWA GAME DA BACEWAR JANAR IDRIS ALKALI
Daga datti Assalafiy
Bayan rundinar sojin Nigeria ta kama wasu mutane 13 da akace sunga lokacin da ake tura motar Janar Idris Alkali a cikin kududdufi kuma sun san mutanen, rundinar sojin ta mika wadanda ake zargin ga rundinar 'yan sanda domin bincike
Jiya rundinar 'yan sanda reshen jihar Pilato ta fitar da sanarwa tana neman wasu mutane 'yan kabilar berom guda 8 da ake zargin sune suka hallaka Janar Idris Alkali, cikin wanda ake nema ruwa a jallo har da Sarkin Dura, ga sunayensu kamar haka:
👇
1- Da Chuwang Samuel 'dan shekara 28 yana da launin baki, kuma dogo ne, babu zane a fuskarsa, 'dan kabilar berom, yana jin yaren berom, hausa da ingilishi, ga nambar wayanshi kamar haka 08063644429
2- Nyam Samuel amma yafi shahara da sunan "Soft Touch" 'dan shekara 25, yana da launin baki, dogo ne, babu zane a fuskarsa, 'dan kabilar berom yana jin yaren berom, hausa da turanci
3- Mathew Warng yafi shahara da "Amesco" 'dan shekara 27, baki ne kuma dogo, a makogoronsa akwai abinda ake cewa zakaran Allah (Adams apple) 'dan kabilar berom, yana jin yaren berom, hausa da turanci
4- Pam Gyang Dung yafi shahara da sunan "Boss" 'dan shekara 53, yana da wushirya, dogo ne, babu zane a fuskarsa, yana da sanko a kansa, manomi ne, 'dan kabilar berom, yana jin yaren berom, hausa da turanci
5- Chuwang Istifanus Pwajok Stephen yafi shahara da sunan "Tifa" 'dan shekara 46 yana da haske, dogo ne, kuma yana sana'ar kasuwanci, babu zane a fuskarsa, 'dan kabilar berom yana jin yaren berom, hausa da turanci
6- Timothy Chuan 'dan shekara 26, yana da haske, dogo ne, babu zane a fuskarsa, kuma yana da aure, direban tifa ne, ga nambar wayanshi 09081177573 'dan kabilar berom ne, yana jin yaren berom, hausa da turanci
7- Moses Gyang yafi shahara da sunan "Boss" 'dan shekara 25, yana da haske, yana da tsayi, akwai aski irin na afro a kansa, babu zane a fuskarsa, yana da aure, 'dan kabilar berom ne, yana jin yaren berom, hausa da turanci
8- Yakubu Rap 'dan shekara 52, baki ne, yana da tsayin mita 1.66 yana da sanko a kansa, babu zane a kansa, shine Sarkin Dura, yana da aure da yara, dan kabilar berom ne, yana jin yaren berom, hausa da turanci
Rundinar 'yan sandan Nigeria tana rokon al'umma duk inda akaga wadannan mutane guda takwas a kai rahoto ga ofishin 'yan sanda mafi kusa, ko kuma a kira wadannan nambobin waya kamar haka 07059473022, 08038907662, 08075391844, 09053872296
Muna rokon Allah Ya tona musu asiri a duk inda suka buya cikin wannan duniya Amin

No comments:

Post a Comment