Buhari yayi alkawarin dawo da Leah Sheribu


Shugaban yayi wannan alkawarin ne yayin da tattauna da mahaifiyar Leah Sheribu ranar Laraba 3 ga watan Oktoba ta hanyar kiran wayan salula.

Shugaba Muhammadu Buhari yayi alkawarin dawo da dalibar makarantar Dapchi daya tilo dake garkame a hannun mayakan Boko haram, Leah Sharibu.

Shugaban yayi wannan alkawarin ne yayin da tattauna da mahaifiyar dalibar mai suna Rebecca Sharibu, ranar Laraba 3 ga watan Oktoba ta hanyar kiran wayan salula.
Labarin haka ya fito ne a sakon da ya wallafa a shafin sa na Twitter.

Yana mai cewa  "Yau nayi magana da Mrs Rebecca Sharibu, domin in jadada aniyarmu ta dawo da 'yarta gida lami lafiya. Dukan 'yan Najeriya suna yiwa iyalin Sharibu da kuma iyalan dukan wadanda har yanzu suke tsare addu'oi. Zamu yi iyaka kokari mu dawo da su".
Ko a cikin watan Agusta an ji muryar Leah Sheribu a cikin wani faifai tana kiran gwamnatin tarayya da ta gaggauta wajen ganin wadanda ke tsaron ta sun sake ta.
Za a iya tuna cewa, an sace Leah Sharibu ne ranar goma sha tara ga watan Fabrairu wannan shekarar, tare da wadansu dalibai mata dari da goma a makarantar Sakandaren ta Dapchi,  ranar 21 ga watan Maris, kuma kungiyar Boko Haram ta maido da 'yammata dari da hudu.
Bisa ga bayanan daliban, abokansu biyar sun rasu sakamakon azaba da suka sha lokacin da aka sace su, suka kuma bayyana cewa, kungiyar kuma taki sakin Leah ne saboda da taki Musulunta.

No comments:

Post a Comment