Zaben shiga majalisar dokokin tarayya: Gwamnoni masu barin gado 7 na APC dake takarar Sanata a zaben 2019


Ga wasu daga cikin gwamnonin jam'iyar APC masu barin gado da suka fito takarar kujerar majalisar dattawa a zaben 2019 karkashin jam'iya mai mulki kamar haka

Komawa zauren majalisar tarayya bayan kammala wa'adi biyu a saman kujerar mulkin jiha ba abu bane sabo tsakanin yan siysan Nijeriya.

Yayin da kasar ta tsangwama cikin magagin siyasa gabanin zaben 2019, wasu daga cikin gwamnoni masu barin gado sun karkata arkallar su zuwa majalisar dokokin tarayya domin cigaba da anniyarsu na jagorantar jama'ar jihar da suke wakilta.
Ga wasu daga cikin gwamnonin jam'iyar APC masu barin gado da suka fito takarar kujerar majalisar dattawa a zaben 2019 karkashin jam'iya mai mulki kamar haka;

Kashim Shetima

Gwamnan jihar Borno ya lashe zaben fidda gwani na APC na takarar majalisa mai wakiltar yankin Borno ta tsakiya.
Ya doke abokin takarar sa Ali Wurge bayan da ya samu kuri'u 2735 sabanin kuri'u 5 da abokin takarar sa ya samu.

Tanko Al-makura

Shima gwamnan jihar Nasarawa zai nemi shiga zauren majalisar dattawa karkashin jam'iya mai mulki.

Ibrahim Gaidam

A jihar Yobe, gwamnan mai barin gado zai maye gurbin Bukar Abba, a majalisar dattawa karkashin inuwar APC. Ya samu kuri'u mafi rinjaye a zaben fitar da gwani da jam'iyar tayi a jihar.

Abdul'aziz Yari

Duk da cewa an dage ranar sake gudanar da zaben fidda gwani na jihar Zamfara, gwamnan shine wanda zai wakilci APC a zaben 2019 a takarar dan majalisar dattawa mai wakiltar yankin yammacin jihar Zamfara. Tsohon gwaman jihar, Ahmad Sani Yarima, ya soke sake takarar kujerar domin baiwa gwamnan dama.

Rochas Okorocha

Gwamnan jihar Imo zai nemi ya haye majalisar dokokin a zaben 2019 bayan kammala wa'adin sa na biyu a matsayin gwamnan jihar.

Ibikunle Amosun

Gwamna Ogun yayi nasarar zama dan takarar APC bayan da ya samu kuri'u 190, 987 cikin 201, 620 da aka kada.

Abiola Ajimobi

Gwamnan jihar Oyo kuma surukin takwarar sa na jihar Kano ya lashe zaben APC na zama dan takarar ta a zaben 2019. Ya samu kuri'u 2,659 yayin da babban abokin takarar sa, Dakta Fola Akinosun, ya samu kuri'u 168.

No comments:

Post a Comment