Abin Da Ya Sa Muke So A Yi Doka A Kan Jakai — Dan majalisa

Abin da ya sa muke so a yi doka a kan jakai — Dan majalisa

Majalisar dokokin Najeriya, za ta gudanar da zaman sauraron ra’ayoyin jama’a kan wani kudurin doka da zai ba da damar haramta fitar da jakuna ko sassan jikinsu zuwa kasashen k’etare.

An dai yi wa kudurin dokar karatu na biyu a ranar Talata.

Ana fitar da jakunan Najeriya zuwa wasu kasashe musamman China inda rahotanni ke cewa ana amfani da wasu sassan jikinsu musamman fatunsu domin hada magungunan gargajiya da kuma kara wa abinci sinadarai.Haka kuma a Najeriya, ana samun wasu al’umomi da kan yanka jakuna don cin nama.

Honorobul Garba Datti Muhammad, dai shi ne ya gabatar da kudurin dokar, inda ya shaida wa BBC cewa, saboda barazanar karewar jakunan a Najeriya, ya sa ya zamo wajibi ayi dokar da za ta kare jakunan.

Dan majalisar ya ce, saboda bukatar jakunan da ake da ita musamman a kasashen wajen, yanzu farashin jakunan ya tashi, inda talaka ma ba zai iya siya ba.

Honorobul Garba Datti Muhammad, ya ce jakuna na da matukar amfani a Najeriya, domin duk suke da juriyar shiga duk wasu lungu da sako da mota ba ta iya shiga ta kai kaya.

No comments:

Post a Comment