Aiki Za Muyi Da Hadiza Ba Bautar Allah Ba -El Rufa`i

Aiki Za Muyi Da Hadiza Ba Bautar Allah Ba – El Rufa’i

“Don na zabi Musulma a matsayin wacce zamu yi takara tare, mutane suna ta guna-guni. Amma ya kamata su sani, gidan gwamnati ba wurin bautar Allah bane, mun zo nan ne domin mu yiwa al’umma aiki.”

“Mutanen da suke wannan guna-gunin, mafi yawansu ba su zabe ni ba tun farko. A don haka, da ya kamata ne su fara murna in dai a ra’ayinsu ban yi zabi mai kyau ba? To me yasa suke bakin ciki?” Ya tambaya.

-Inji Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai a lokacin da yake magana da al’ummar karamar hukumar Sanga a ziyarar da suka kai masa na nuna godiya bisa yadda ya dauki ‘yarsu a matsayin mataimakiyarsa a zaben da za a yi na 2019.

No comments:

Post a Comment