Amarya Da Ango Sun Mutu Ranar Da Aka Daura Musu Aure


Wata amarya da angonta daga jihar Texas ta Amurka sun mutu sakamakon hatsarin da jirgi mai saukar ungulun da ke dauke da su ya yi lokacin da suke kan hanyarsu ta komawa gida daga wurin liyafar aurensu, in ji wasu jami'ai.

Will Byler da Bailee Ackerman Byler dukkansu dalibai ne a Jami'ar Sam Houston. Wata jaridar dalibai ce ta soma ba da rahoton hatsarin nasu.

Sun yi hatsarin ne a kusa da Uvalde, kimanin mil 85 da yammacin San Antonio.

Mutanen da suka halarci liyafar tasu sun yi ta mika ta'aziyyarsu a sakonnin da suka wallafa a shafukan zumunta.

"Na yi matukar kaduwa!" In ji wani abokin ango a sakon da ya wallafa a Facebook, yana mai karawa da cewa matukin jirgin ma na cikin wadanda suka mutu.

A wata sanarwa da shugaban daliban jami'ar ya fitar, ya ce za a rika tunawa da ma'auraan saboda kirkinsu

No comments:

Post a Comment