An Gurfanar Da Dan Nijeriya Da Ya Damfari Amurkawa 250 A Gaban Kotu

An gurfanar da wani dan Nijeriya mai suna Osmond Eweka a wata kotu dake Manhattan a makon da ya gabata, bisa zargin damfarar Amurkawa masu neman aiki na dubban daloli.
Wanda ake zargi ya yi wa Amurkawan alkawarin zai sama musu aiki. Matashin mai shekaru 31 ya roki kotu da ta ba shi dama ya ziyarci Nijeriya wajen bikin murnar bukin ranar zagayowar haihuwar dansa.
Eweka da abokinsa Kamel McKay ana zargin su ne da samar da ayyukan karya ga kamfanoni, inda suke amfani da shafukan yanar zigo wajen neman mutane.
Suna magana da mutane, inda suke sanya su biyan kudin ladan aiki wanda ya kai tsakanin dala 300 ko kuma dala 700.
Wadanda ake zargin sun yi ta sa masu neman aiki yin kasuwancin da babu riba, saboda aikin baya samuwa a wajen su.
Eweka ya musanta tuhumar da ake masu na sata da damfara a watan Yuli.
Lauya mai kara ya bayyana cewa, aikin otel ne Eweka da kuma McKay suke yi ma wanda suka damfara alkawari.
A bayanin da kotu ta samu shi ne, Eweka da kuma McKay suna amfani ne da filin ginin Empire da kuma wani gini da ke Fifth Abenue wajen kirkiran ayyukan kamfani guda biyu na garya wanda suka hada da Stamford Consulting Firm da kuma Howard Consulting Group.
Suna amfani da sunayen karya, a cewar jami’an tsaron New York. Eweka yana amfani da Sean Jackson yayin da McKay yana amfani da Tyrone Hayes.
#Hausaleadership

No comments:

Post a Comment