An Kori Mataimakin Shugaban Jam`iyyar Apc Na Kasa

JAM’IYYAR APC ta Kasa ta Kori Barr. Inuwa Abdulkadir daga mukamin sa na Shugaban Jam’iyyar Mai Kula da Yankin Arewa Maso Yamma Akan Zargin sa, na Yin Angulu da Kan Zabo.
Barr. Inuwa Abdulkadir Wanda Ake Ganin Yana Gaf da Gaf da Gwamnan Jihar Sakkwato Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal. Wanda yayi chanjin sheka daga jam’iyyar APC Mai mulkin kasa zuwa Babbar jam’iyyar adawa ta PDP, kuma Suka Raba Gari da Jagoran Jam’iyyar APC na Jihar Sakkwato. Sanata. (Dr) Aliyu Magatakarda Wamakko. Kuma Jigon Jam’iyyar na Kasa.
Da Yake Zantawa da Manema Labarai ta Wayar Hannu, Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Sakkwato Hon. Isah Sadiq Achida Ya ce An Kori Inuwa Abdul-Kadir ne, Sakamakon Kama Shi da Laifukkan Yin Angulu da Kan Zabo, ba ko Sau Daya ba. Kamar Yin Taruruka Daban Daban, Rashin Biyayya ga Jagororin Jam’iyyar APC da Kuma Yin Fatali da Lamurran Jam’iyyar.
Shugaban ya Bayyana Cewa Korar sa, Daga Jam’iyyar ta Biyo Bayan Bin Ka’idojin da Suka Dace Gabanin Korar, Kana Kuma da yin Kememe da Yayi ga Bayyana Agaban Kwamitin da Aka Kafa Masa Ko Kuma ya Aiko da Wakilin sa.
Shugaban Jam’iyyar ya ci Gaba da Cewa Ambi Dukkan Matakan da Tsarin Mulkin Dokokin Jam’iyyar ya Shata, Akowane Mataki. Matakin Korar dai, ya Fara ne. Tun Daga Mazaba, Karamar Hukuma, Inda Uwar Jam’iyyar ta jihar Sakkwato. ta Aminta da Korar, Sannan Aka Turawa Uwar Jam’iyyar ta Kasa.
Laraba. 07/11/2018.
Muna fatan samun Maye gurbin sa da Dan jam’iyyar APC Mai nagarta Domin cin nassarar zaben dake tafe.
Northwest APC social Forum.

No comments:

Post a Comment