An Zo Wurin: Hukumar ICPC Za ta Binciki Oshiomhole A Kan Zargin Badakala

An zo wurin: Hukumar ICPC za ta binciki Oshiomhole a kan zargin badakala

A jiya , Laraba, ne hukumar yaki da cin hanci da binciken almundahana (ICPC) ta bayyana cewar za ta binciki zargin almundahana da ke yiwa shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole.

Wannnan mataki na hukumar ICPC na zuwa ne kasa da mako guda da gayyatar da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta yiwa Oshiomhole a kan zarginsa da almundahana yayin gudanar da zabukan cikin gida na jam’iyyar APC.

Kakakin hukumar ICPC, Rasheedat Okoduwa, ce ta bayar da wannan tabbaci ga kungiyar ‘Coalition 4 New Nigeria’ yayin da su ka je ofishin ICPC domin neman hukumar ta binciki Oshiomhole.

Dandazon ma su zanga-zanga, karkashin jagorancin Stanley Onukwufor, dan gwagwarmayar neman ‘yanci, sun ziyarci hedkwatar ICPC dauke da takardun neman a binciki Oshiomhole tare da yin kira ga shugaba Buhari da ya tsige shi.

Da take jawabi ga ma su zanga-zangar, Rasheedat, ta ce,”babu abinda zai hana mu bincike shi matukar kun kawo mana korafin ku arubuce.”

“Sai dai ina son ku sani cewar jama’a na kawo ma na korafi kowacce sa’a yayin da mu ke Ofis, a saboda haka mu na bin abin ne a layi.
“Ba zamu bar korafin daya fi na ku dadewa ba domin kuna zanga-zanga.

“Har yanzu batun zabukan fitar da ‘yan takara na jam’iyyar APC na cigaba da tayar da kura da jawo musayar yawu tsakanin Oshiomhole da wasu ‘yan jam’iyyar ta APC dasu ka hada da gwamnoni, ministoci, da sanatoci.

No comments:

Post a Comment