Alhamdulillahi :Anyo Belin Yan Biyun Zamfara

Assalamu Alaikum yan uwa masu Albarka, Allah yasa an kubutar da Hasana da Hussaina da akayi garkuwa da su a Dauran da ke karamar hukumar Zurmi jihar Zamfara
Da haka kungiyar Muryar Talaka-Reshen Jahar Zamfara ke matukar Godiya ga daukacin wa’danda suka bada tallafi kudu da Addu’o’in wurin kubutar da su
Godiya Ta mussamman ga Sanata Kabiru Garba Marafa
Godiya ta mussamman ga yan uwa masu Albarka da suka dage wurin yada wannan Iftila’i har Allah ya kubutar da su
Daga karshe shugaban kungiyar muryar talaka reshen jahar Zamfara
Hafizu Balarabe Gusau yana shedawa daukacin yan uwa masu Albarka an rufe karbar tallafin kudi da yawun ceto yan 2,
Muna rokon Allah ya kubutar da daukacin mutanen da ke hannun masu garkuwa da mutane a sassa daban-daban na kasar nan
Daga M Baban Yusurah Gusau a madadin yayan kungiyar muryar talaka reshen jahar Zamfara.

No comments:

Post a Comment