Atiku Ba Zai Kai Ko’ina A Zaben 2019 Ba Inji – Tinubu

Uban jam’iyya mai mulkin Najeriya ta APC, tsohon Gwamnan Legas Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ce dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ba zai kai ko ina ba a zaben 2019.
Tinubu ya bayyana hakan ne bayan ganawarsa da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a  fadar Shugaban kasar. Atiku ya koma ya sasanta da magoya bayansa saboda ‘yan Najeriya ba zasu zabe shi ba a zabe na gaba.
Tinubu ya mayar da martani game taron Atiku ya yi da shugabannin jam’iyyar PDP a birnin Dubai akan yadda zasu tunkari zaben 2019

No comments:

Post a Comment