Ba Za Ku San Akwai Na`urorin Bincike Ba Sai An Yi Garkuwa Da Matar Babba A Nijeriya

Ba Za Ku San Akwai Na’urorin Bincike Ba Sai An Yi Garkuwa Da Matar Shugaban Kasa Ko Gwamna Ko Babba A Nijeriya
Daga Abdurrahman Abubakar Sada
Mu masana bincike ne na zamani, kuma ba za ku san akwai na’urorin bincike a kasar nan ba, yau sai an ce an yi garkuwa da uwa, ko mata, ko ─Ćan shugaban kasa, ko gwamna, ko wani babban mutum a Nijeriya, a lokacin za ku tabbatar akwai tsaro da bincike.
Talaka ya yi hakuri kawai har Allah ya kai mu kiyama, domin karbar hakkinsa. Komawa ga Allah a cikin halin damuwa da bakin ciki shine mafita.
Babu wani mutum da Allah zai damka masa jagorancin wasu mutane, ya mutu yana mai ha’intarsu, face sai Allah ya haramta masa shiga Aljanna.
Allah ka kaskanta miyagun shugabanni, ka raba su da kujerunsu suna kaskance tun a nan duniya.

No comments:

Post a Comment