Ba Zamu Iya Biyawa Kungiyar ASUU Bukatar Tar Su Ba A Yanzu

Gwamnatin tarayya ta bukaci kungiyar ASUU da ta kara hakuri akan bukatun da take bukatar a biya mata, saboda a cewar gwamnatin ba za ta iya biyan wadannan bukatun ba a halin yanzu, Ministan ilimi, Malam Adamu Adamu ne ya shaida hakan a yayin ganawa da manema labarai a garin Abuja. Ministan ya bayyan matsalolin a matsayin tsofaffin matsaloli, wanda tun lokacin gwamnatin Umaru Musa Yar’adua, ASUU din ta shigar da wadannan bukatun, ministan ya ce faduwar farashin gangar mai ya sa gwamnatin tarayya ta gaza wajen cika wadannan bukatun na kungiyar ASUU.
Adamu ya ce gwamnatoccin baya sun yi wa kungiyar wadannan alkawuran ne a daidai lokacin da farashin gangar danyen ya yi tashin gwauron zabi, inda akayi wa kungiyar alkawarin sakin kudaden gudanarwa ga jami’o’in da adadin shi ya kai Naira tiriliyan 1.3 a cikin shekaru shida. ‘Alkawuran da gwamnatin marigayi Umaru Musa ‘Yar’adua ta yi wa kungiyar ASUU na sakar wa jami’o’in kasar na kudade da yawansu ya kai tiriliyan 1.3, ta yi ne a daidai lokacin da gangr danyen mai ta yi mugun tsada a kasuwar duniya, don haka
Nijeriya ta na da damar cika wannan alkawarin a wancan lokacin, amma daga baya farashin danyen man ya fadi warwas, wanda hakan ya sanya kasar nan ta shiga cikin matsalar tattalin arziki, don haka abu ne mai kamar wuya a iya biyan wadannan bukatun a yanzu.’ Inji Adamu Kungiyar ASUU, ta zargi gwamnatin tarayya da kin cika alkawarin da ta dauka har sau uku, don haka ya zama dole ga kungiyar ta shiga wannan yajin aikin, zuwa yanzu babu alamar wata tattaunawa a tsakanin kungiyar malaman da gwamnatin tarayya, duk ana ganin za a iya tattaunawar a satin da zamu shiga.

No comments:

Post a Comment