Babu Wani Sauran Mai Tunani a Jam`iyyar PDP -Gwamna El-rufai

Babu Wani Sauran Mai Tunani a Jam’iyyar PDP – Gwamna El-rufai

Gwamnan jihar Kaduna Gwamna Nasiru El-Rufai ya mayar da martani ga jam’iyyar inda ya yi kaca-kaca da jam’iyyar da cewa babu sauran wani mai tunani da ya rage a jam’iyyar a yanzu.

Gwamnan dai ya mayar da martani ga jam’iyyar ta PDP ne wanda da a farko ta caccake shi biyo bayan kalamansa wanda ya ambaci tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi da ke zaman mataimaki ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2019.

Gwamna El-Rufai ya yi kalamai akan Mista Peter Obi inda yace shi mai tsananin kabilanci ne, ya jawo cece-kuce da zafafan kalamai daga al’ummar Nijeriya din wanda hakan ne ma ya sa jam’iyyar ta PDP ta fitar da sanarwa dauke da martani zuwa ga gwamnan.

The post Babu Wani Sauran Mai Tunani a Jam`iyyar PDP -Gwamna El-rufai appeared first on ArewaBlog.Com™.

No comments:

Post a Comment